✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Italiya zai hada kai da NCC don karfafa bangaren tarho

Kamfanin Sadarwa na kasar Italiya mai suna Italia Sparkle (TIS) ya ce yana neman hadaka da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) domin samar da cikkaken…

Kamfanin Sadarwa na kasar Italiya mai suna Italia Sparkle (TIS) ya ce yana neman hadaka da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) domin samar da cikkaken yanayin sadarwa da taka rawar gani ga fannin  sadarwa.

Mataimakin Jakadan Italiya, Mista Tarek Chazli, ya bayyana haka lokacin da suka kai ziyara a babban  ofishin NCC  da ke Abuja.

Chazli, wanda ya jagoranci ziyarar, ya bayyana cewa kwararru a fagen harkar sadarwa, sun bayyana Najeriya a matsayin kasa a Afirka da za su saka jari kan sadarwa kuma su taka rawar gani a fannoni daban-daban.

Ya ce sun gano Najeriya da Italiya suna da masu amfani da waya domin sadarwa, kuma ya ce Najeriya tana daga cikin na farko masu amfani da waya domin sadarwa, tsara hanyar kasuwanci da muhimmanci  cibiya.

“Haka dai ya bayyana Najeriya a matsayin wajen da za su yi kasuwanci, kuma za su kara darajar kasuwanci a Najeriya,” inji shi.

Miss Stefano Olibieri, Shugaban Kasuwanci na Afirkan  da yankin Gabas ta Tsakiya, ya ce shi ne kamfanin da yake taka rawar gani ga kasar Italiya da Brazil da Burundi da bangarorin kasuwanci na sadarwa.

Ya ce Shigowarta kasuwannin Najeriya ta cika alkawari wajen ganin canja yanayin sadarwa.

Olibieri, ya ce kamfanin tana da babban shi ne da take yi don kasashe su samu yanayin Intanet mai kyau da kawo kasuwanci don cigaban ’yan Najeriya.

“Kamfanin tana kokari wajen samar da tsaro ga tsarin sadarwa na Intanet.

“Da yawan masu amfani da tsarin cibiyar tura sako suna da TIS.,”  inji shi.

Mista Adeleke Adewolu, (ECSM), NCC ya bayyana farin cikinsa ga tawagar da suka kai ziyarar kuma ya gode wa TIS bisa ga nuna kwadayinsu na shigowa kamfanonin sadarwa.

Adewolu  ya ce wa kungiyar da suka ziyarce su NCC tana kokari wajen ganin samar da ingantacen Intanet a kasar nan.

Ya ce ECSM, ya yi alkawarin kai sako ga TIS zuwa ga Shugaban NCC Farfesa Umar Dambatta da sauran mukarabansa domin amincewa.

Ya bada umarni ga shugaban ba da izini da tabbatarwa na hukumar kan tattaunawa da TIS ga rubutowa da suka yi, kafin ba su izini.

“NCC ta bada izini da kayan aiki ga kamfanoni kan hanyar zuwa dukkan kananan hukumomin Najeriya.

“Kana, za a bayyana daga Ministan Sadarwa da Kasuwanci na Zamani, Dokta Ali Ibrahim Pantami zai bada bayani kan yarda za a fadada tsarin kwamfuta a Najeriya,”  inji shi.