✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Jaridun Media Trust ya karrama ma’aikatansa 41

Rukunin kyaututtukan da aka ba da kyautar sun hada da kwazo da nagarta da kuma dadewa a aiki.

Kamfanin Media Trust, da ke wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya, a ranar Alhamis ya karrama ma’aikatansa 41 da suka nuna kwazo da nagarta da ma dadewa a aikin kamfanin.

Bikin wanda aka gudanar a hedikwatar kamfanin da ke Abuja, ya samu halartar Daraktocin Hukumar Gudanarwar kamfanin wadanda Shugabansu kuma Shugaban Kungiyar Masu Gidajen Jarida ta Najeriya, NPAN, Mallam Kabiru Yusuf ya jagoranta.

Hukumomi da ma sauran ma’aikatan kamfanin da dama ne suka halarci bikin.

A cewar Babbar Manajar Sashen Kula da Ma’aikata da Harkokin Gudanarwa, Hajiya Hadiza Ibrahim Bala, an yi shirya shi ne domin karrama ma’aikatan da suka yi zarra a shekarun 2019 da 2020.

Abdullateef Aliyu, wakilin jaridar Daily Trust a Legas da ma Aliyu AbdulHamid na bangaren baitil malin kamfanin a babban ofishinsa da ke Abuja, sun samu Karramawar Shugaban Kamfanin wanda yake kunshe da kudi N250,000 tare da takardar karin girma.

Har wa yau, Shugabar Sashen Labarai ta kamfanin a Kaduna, wacce kuma ita ce ke lura da yankin Arewa ta Tsakiya, Lami Sadiq Mohammed da Iyorah Eucharia daga Sashen Tallace-tallace na kamfanin a Legas dukkaninsu sun sami Lambar Yabo ta Nagartar Aiki tare da kudi N150,000 da ma takardar karin girma.

Babban Jami’in Kamfanin, Malam Nura Mamman Daura da Mukaddashiyar Edita, Iyaji Stella da Sakataren kamfanin Malam Muhammad Kabiru Bala da ma Editan Shafukan Siyasa na jaridar Malam Ismail Mudashir da wadansu ma’aikatan 26 dukkaninsu sun samu lambar yabo ta share shekara 10 suna aiki da kamfanin.