✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin shinkafar Kano ya ci gaba da aiki duk da samamen ‘yan sanda

Duk da ce-ce-ku-cen da aka yi ta yi a kan samamen da ‘yan sanda suka kai a kamfanin sarrafa shinkafa na Popular Rice Mills da…

Duk da ce-ce-ku-cen da aka yi ta yi a kan samamen da ‘yan sanda suka kai a kamfanin sarrafa shinkafa na Popular Rice Mills da ke Kano tare da ceto ma’aikata 126, Aminiya ta gano cewa har yanzu kamfanin na ci gaba da aikinsa kamar yadda ya saba.

Wannan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin ma’aikatan suka yi zargin cewa sun yi kokarin su koma aiki kamfanin amma aka hana su shiga.

To sai dai wani jami’i a kamfanin, Hassan Sufi ya shaida wa Aminiya cewa babu kamshin gaskiya a ciki, yana mai cewa ko lokacin da ‘yan sanda suka kai samame kamfanin ba su rufe shi ba.

Ma’aikatan da aka ceto bayan shafe kimanin watanni uku a kulle cikin kamfanin sun ce wasu daga cikin abokan aikinsu sun yi yunkurin shiga kamfanin da safiyar Laraba don komawa bakin aiki amma aka hana su shiga.

Wasu daga cikin ma’aikatan kamfanin da aka sami nasarar cetowa

“Bayan kulle mu na tsawon watanni uku muna aiki ba dare ba rana, ba kuma tare da biyan mu hakkokinmu yadda ya kamata ba, ‘yan sanda sun zo sun ceto mu.

“Amma wasu daga cikinmu sun yi kokarin su shiga kamfanin yau (Laraba) amma an hana su”, inji Alhaji Yahaya, daya daga cikin ma’aikatan.

Ya kuma yi zargin cewa kamfanin ya gaza cika alkawarin da ya yi musu na biyansu karin kudi Naira dubu biyar-biyar a kowane mako sakamakon kullen da ya yi musu suka ci gaba da aiki.

Kazalika, wani wanda aka ceto mai suna Mukhtar Abubakar ya ce suna tsoron yiwuwar kamfanin ya sallame su daga aiki, yana mai cewa a yanzu haka masu kamfanin sun dage kan cewa ma’aikata 20 kawai suke bukata a cikinsu.

To sai dai jami’in kamfanin ya karyata duk zarge-zargen

“Ko a lokacin da ‘yan sanda suka kawo samame don ceton ma’aikatan ranar Litinin fa ba wai kulle kamfaninmu suka yi ba. Ba mu taba rufe kofarmu ba, ba aikin da ya tsaya a ciki.

“Maganar da nake da kai yanzu haka yau (Laraba) mun yi aiki da safe, masu aikin rana kuma sun karbe su, zuwa dare kuma wasu za su canje su.

“A zahirin gaskiya ko a ranar Litinin ma da kuka yi ta yada labarin kwana muka yi muna aiki. Ban san wa ya ce wai ‘yan sanda sun rufe kamfaninmu ba. Ba gaskiya ba ne”, inji jami’in kamfanin.

Kamfanin na da damar ci gaba da aiki

Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce kamfanin na da damar ci gaba da aiki tun da dai jami’ansu da suka ceto mutanen ranar Litinin ba su garkame shi ba.

Sai dai ya ce suna ci gaba da fadada bincike, kuma da zarar sun kammala za su yi wa jama’a karin bayani.

A gefe daya kuma, wata kungiya mai rajin kare hakkin dan Adam wadda ita ce ta ankarar da ‘yan sanda kan kulle leburorin tun da farko mai suna Global Human Rights Network, ta ce za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin kamfanin ya biya ma’aikatan da aka ceto dukkannin hakkokinsu.

Karibu Yahaya Lawan na Global Human Rights Network

“Za kuma mu tabbatar kamfanin bai sallami ko da mutum daya daga bakin aikinsa ba”, inji jagoran kungiyar, Karibu Yahaya Lawan, a tattaunawarsa da Aminiya.