✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Twitter ya amince da tayin Elon Musk na sayen shi kan $44bn

Ya bukaci kamfanin ya kawo sauye-sauye da suka hada da shafe shafukan bogi

Hukumar gudanarwar shafin sada zumunta na Twitter ta amince da tayin sayen shafin da attajirin duniya, Elon Musk, ya yi a kan zunzurutun kudi har Dalar Amurka biliyan 44.

Musk wanda ya yi tayin ba-zata kasa da sati biyu da suka gabata ya ce shi ne wanda ya fi dacewa ya bude abubuwan ban al’ajabi da manhajar sada zumuntar ta kan shi.

Ya kuma bukaci kamfanin da ya kawo sabbin sauye-sauye da suka hada da shafe shafukan bogi da sassauta tsauraran dokokinsu.

Da fari dai kamfanin na Twitter ya yi watsi da tayin na Musk, amma yanzu ya ce zai ba wa masu hannun jari a kamfanin damar kada kuri’a kan wannan bukata ta shi.

Elon Musk dai shi ne mutumin da ya fi kowa kudi a duniya kamar yadda mujallar Forbes ta rawaito, da fiye da zunzurutun kudi har Dala biliyan 276.

Attajirin ya ce ’yancin tofa albarkacin baki shi ne tubalin kowane tsari na Dimikuradiyya, kuma Twitter guri ne da ke ba da damar hakan, domin ana tafka muhawara kan muhimman lamuran da suka shafi goben ’yan Adam.

Yayi wannan furucin ne a jawabinsa na bayyana wancan tayin.

“Zan sake inganta Twitter fiye da a baya ta hanyar kara sabbin abubuwa, ciki har da wanda zai kara karfin yarda tsakanin kamfanin da mutane, da kuma tabbatar da cewa dan Adam ne kadai ke amfani da shi,” inji Elon Musk.

A nasa bangaren, Bret Taylor, Shugaban kamfanin Twitter ya ce sun gama bin duk matakan duba bukatar Mista Musk gare su.