✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kanada ta hana baki daga Najeriya shiga kasarta saboda Omicron

Kawo yanzu ba a san iya hadarin kwayar cutar ba, ko kuma ba ta jin rigakafin cutar COVID-19.

Gwamantin kasar Kanada ta rufe zirga-zirgar matafiya a tsakaninta da Najeriya bayan bullar nau’in Omicron na cutar COVID-19 a Najeriyar.

Kanada wadda baki daga Najeriya ke yawan zuwa ta sanar da haka ne a safiyar Laraba, sa’o’i kadan bayan an gano mutum biyu masu dauke da cutar a Najeriya.

Kawo yanzu kasashe 10 ke nan Kanada ta rufe zirga-zirgar matafiya a tsakaninta da su saboda bullar kwayar cutar ta Omicron a cikinsu.

Kasashen su ne Najeriya, Afirka ta Kudu, Masar, Zimbabwe, Mozambique, Malawi Namibia, Lesotho, Botswana da kuma Eswatini.

Ministan Sufurin Kanada, Omar Alghabra, ya ce kasar za ta sanya takunkumin wucin gadi ga duk bakin da suka ziyarci kasashen a cikin kwana 14 da suka gabata.

Ya kara da cewa ’yan asalin kasar Kanada da halastattun mazauna kuma da suka ziyarci kasashen sai an yi musu gwaji, ko da kuwa sun riga sun karbi allurar rigakafin COVID-19 kafin su samu izinin shiga kasar.

A karon farko kuma an gano wani mutum mai dauke da kwayar ta Omicron a yankin British Columbia, bayan dawowarsa daga Najeriya.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana Omicron a matasyin “babbar barazana” a duniya da ke iya yaduwa.

Kawo yanzu dai ba a tantance iya hadarin kwayar cutar ba, hakazalika ba a san ko ba ta jin rigakafin cutar COVID-19 ba.