✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kane ya kamo Andy Cole a yawan cin kwallaye

Kane ya koma mataki na uku a jerin mafiya cin kwallaye a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Dan wasan gaban Tottenham Hotspur, Harry Kane ya ci kwallo 201 tun fara sana’ar tamaula, kuma 187 a gasar Firimiyar Ingila.

Hakan na nufin dan wasan na tawagar Ingila ya yi kan-kan-kan da Andy Cole a mataki na uku a jerin mafiya cin kwallaye a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Wannan na zuwa ne yayin da Tottenham ta je ta doke Nottingham Forest 2-0 a wasan mako na hudu a gasar Firimiyar Ingilar da suka fafata ranar Lahadi.

Harry Kane ne ya ci kwallayen biyu ya kuma barar da bugun daga kai sai mai tsaron raga, inda Tottenham ta yi wasa hudu a jere ba tare da rashin nasara ba.

Bayan kwallo 187 da ya zura a raga a Firimiyar Ingilar, ya kuma ci tara a Championship da kuma biyar a gasar League One.

A halin yanzu dai Alan Shearer ne kan gaba mai kwallaye 260 da kuma Wayne Rooney mai 208 a raga a wasa 491, ya kuma bayar da 103 aka zura a raga.