Kanin Aliko Dangote, Sani, ya rasu | Aminiya

Kanin Aliko Dangote, Sani, ya rasu

Marigayi Sani Dangote
Marigayi Sani Dangote
    Sani Ibrahim Paki

Kani ga babban attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote, wato Alhaji Sani Dangote, ya rasu.

Marigayin dai shi ne mamallakin kamfanin kayan noma da dangoginsu na Dansa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ya rasu ranar Lahadi a wani asibiti da ke kasar Amurka bayan ya sha fama da jinya.

Kafin rasuwarsa, Alhaji Sani ya shafe sama da shekara 30 yana gudanar da harkokin kasuwanci musamman a bangaren masana’antu, kayan noma da harkar mai.

Ya kuma rike manyan mukamai a kamfanoni da dama, ciki har da kamfanin saka na Nigerian Textile da kamfanin alawoyi na Nutra Sweet da kamfanin masakar Dangote Textile da kamfanin lemuka na Dansa da Dangote Farms da dai sauransu.