✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kanin Sarkin Musulmi ya rasu

Kwamishinan Cikin Gidan Jihar Sakkwato kuma kanin Sarkin Musulmi ya rasu

Kani ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Kwamishinan Harkokin Ciki Gida na Jihar Sakkwato, Abdulkadir Jeli Abubakar, ya rasu.

Kanin Sarkin Musulmi, Kwamishinan Harkokin Ciki Gida na Jihar Sakkwato, Abdulkadir Jeli Abubakar, ya rasu.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya rasa daya daga cikin kwamishinonin nasa ne da marecen Alhamis.

Alhaji Abdulkadir ya bar duniya ne bayan wata bakwai da rasuwar Kwamishinan Filaye da Gidaje, Surajo Gatawa.

Margayin mai shekara 64 kane ne ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, kuma ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya da jikoki.

An yi masa sutura kamar yadda shari’ar Musulunci ta shardanta.

Gwamna Tambuwal yana cikin wadanda suka halarci sallar janaza ta margayi.