✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kannywood: Jarumi Ahmad Tage ya rasu

Za a yi jana'izar jarumin da misalin karfe hudu a Kano.

Allah Ya yi wa shararren jarumin barkwancin Kannywood, Ahmad Aliyu Tage rasuwa bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Ayatollahi Tage ne ya sanar da rasuwar jarumin, inda ya ce, “Innanillahi wa inna ilaihir raji’un; Allah Ya gafarta maka. Allah Ya sa karshen wahalar ke nan.

“Allah Ya sa kana cikin ’yantattun bayin da Annabi Muhammad (SAW) zai karbi bakuncinsu; Allah Ya jikan ka baba, ka maye gurbin maihaifi a gareni. Yau ce rana mafi muni a tare da ni. Allah Ya gafarta maka Allah Ya sa ka huta, amin.”

Za a yi jana’izar Ahmad Tage a unguwar Sabuwar Abuja da ke Karamar Hukumar Kumbotso, Jihar Kano da misalin karfe 4 na yamma.

Baya ga barkwanci, marigayi Ahmad Aliyu Tage fitaccen mai daukar hoto ne a masana’antar ta Kannywood wanda aka dade ana damawa da shi.

Tuni jaruman masana’antar maza da mata suka shiga alhini kan rasuwar jarumin tare da masa addu’ar samun rahama daga Ubangi.

Fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu ya wallafa labarin rasuwar Ahmad Tage a shafinsa na Instagram a ranar Litinin, ta hanyar sake wallafa rubutun da Isah Bawa Doro ya yi.

“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, Allah Ya yi wa daya daga cikin masu daukar hoto kuma jarumi a masana’antar Kannywood, Ahmad Tage rasuwa… sakamakon gajeriyar rashin lafiya da ya yi ta fama da ita. Muna rokon Allah Ya jikan sa da rahama,” a cewar sanarwar.