Kannywood: Lawan Ahmed zai tsaya takarar dan majalisa | Aminiya

Kannywood: Lawan Ahmed zai tsaya takarar dan majalisa

Jarumi Lawan Ahmad
Jarumi Lawan Ahmad
    Isyaku Muhammed

Fitaccen jarumin masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Lawan Ahmed zai tsaya takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Katsina domin wakiltar mazabar Bakori.

Jarumin wanda shi ne furodusan shirin ‘Izzar So’ mai dogon zango ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar a shafuka sada zumuntarsa, inda yakan sanya fastar takararsa tare da rakiyar rubutun cewa, “A wajen Allah muke nema.”

A wani rubutun da ya yi na neman takarar, jarumin ya ce, “duk wadanda na lissafa za su iya fitowa takara kowace iri ce, tun daga matakin Shugaban Kasa har zuwa kansila saboda haka mu dai
a wajen Allah muke nema kuma muna neman addu’arku. Na gode,” inji shi, bayan ya lissafa wasu sana’o’i ciki har da fim da a cewarsa dukansu ’yan kasa ne kamar kowa.