✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kannywood: Mahaifin Ibrahim Maishunku ya rasu

Jarumin ya wallafa rasuwar mahafin nasa a shafinsa na Instagrama a ranar Talata.

Allah Ya yi wa mahaifin fitaccen jarumin fina-finan Hausa na Kannywood, Ibrahim Maishunku, Alhaji Labaran Maishunku rasuwa, bayan fama da rashin lafiya.

Jarumin ya sanar da rasuwar mahaifin nasa ne a shafinsa na Instagram.

“Inna Lillahi Wa Inna Ilahi Raji’un, a yau 26 Jan 2021 na yi babban rashi, Allah Ya yi maka afuwa baba.

“Wallahi duk wanda ya tafi cikin aminci ya huta. Allah Ya ba mu hakurin rashin ka baba. Allah Ya sa mu mutu cikin aminci,” cewar Maishunku.

https://www.instagram.com/p/CKhfVswh6Ot/?utm_source=ig_web_copy_link

Alhaji Labaran Maishunku ya rasu ne a ranar Talata yana da shekar 80 a duniya.

Bayan wallafa labarin rasuwar mahaifin nasa, daraktoci, furodusoshi fina-fina da ma jarumai maza da mata daga cikin masana’antar ta Kannywood sun yi ta yi wa Maishunku ta’aziyya.