✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kannywood ta zama kasuwar bukata –  Zango

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam Abdullahi Zango ya bayyana cewa masana’antar fina-finan Hausa ta sauya, inda a yanzu komai ya balbace ta koma kasuwar bukata.…

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam Abdullahi Zango ya bayyana cewa masana’antar fina-finan Hausa ta sauya, inda a yanzu komai ya balbace ta koma kasuwar bukata.

Jarumin ya bayyana haka ne a shafinsa a Instagram a ranar Juma’ar da ta gabata.

Ya ce, Kannywood din yanzu ba kamar ta baya ba ce, ta yanzu sunanta kasuwar bukata, domin mai kudi ko daukaka da ke bude wa mutane hanyar da za su samu kudi shi ne mai fada a ji, “Idan ka rasa daya daga ciki to taka ta kare (a masana’antar), don hakan ya faru da mutane da dama a cikin masana’antar, sannan tarihi ya bar muku littafin da za ku karanta labarin Kannywood,” inji shi.

Ya ce, “Misali, yau ina Ibro? Yau ina Ahmad S. Nuhu? Yau ina Ashiru Nagoma? Yau ina Ar-Rahuz? Yau ina H.R.B? Yau ina Abdul’aziz Dan Small? Yau ina Ahlan? Yau ina Ciroki? Yau ina Usman Mu’azu? Yau ina Abubakar Sani? Yau ina Adamu Nagudu? Yau ina Sadi Sidi? Yau ina Ali Baba Yakasai? Yau ina Ibrahim Danko? Yau ina Zainab Indomie? Duk wadannan mutane ne da aka ci moriyarsu kuma aka juya musu baya, wadansu kuma sun mutu, wadansu kuma ba su da lafiya, don haka amfaninsu ya kare. Wadansu a dalilin wadannan (mutane) suka yi aure, suka sayi mota, suka gina gida, sannan suke ciyar da iyayensu,” inji Zango.

Jarumin ya ce ya rubuta wannan mukala ce saboda ya tunatar da ’yan fim cewa yana da mafita ko an daina daukar fim.

Ya ce, babbar matsalar kuma ita ce matukar Ganduje ya sake hawa kujerar Gwamnan Kano “To wadansu fa zaman Kano ya kare, idan kuma suka zauna to za su yi rayuwa cikin takura da tsoro. Hakazalika idan Abba ya ci hakan ne zai kasance saboda siyasar wannan shekarar ta bambanta da duk wadanda aka yi a baya,” inji shi.

Zango ya ce mutanen Kannywood sun shiga tsaka-mai- wuya ne saboda kwadayi da son zuciya.

Ya ce da ’yan fim za su rika son junansu da kaunar juna kamar yadda suke son ’yan siyasa da za su kai wani mataki na daukakar da ya fi wacce suke samu.

Ya ce, “Ina ma za mu rika son junanmu kamar yadda muke son ’yan siyasa. Ina ma za mu rika yi wa masana’antarmu addu’a kamar yadda muke yi wa ’yan siyasa. Ina ma za mu rika kare mutuncin junanmu kamar yadda muke kare na ’yan siyasa! Ina ma za mu rika tayar da jijiyar wuyanmu idan aka taba iyayen gidammu kamar yadda muke yi wa ’yan siyasa! Ina ma za mu rika kukan bakin ciki idan abokin sana’armu ya shiga mugun hali kamar yadda muke yi wa ’yan siyasa!,” inji Zango.

Jarumin kuma ya ce ya kamata ’yan fim su rika fadin alheran junansu kamar yadda suke fadin na ’yan siyasa, ko su rika tallata wa junansu hajarsu kamar yadda suke tallata jam’iyyar ’yan siyasa.

“Ina ma za mu rika hada kawunanmu kamar yadda muke hadawa idan aka kira mu Billa! Ina ma za mu rika tururuwar zuwa biki da jana’iza da daurin auren junanmu kamar yadda muke tururuwa zuwa wajen kamfen din ’yan siyasa!,” inji Zango.