✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano: An bude makarantun da aka rufe saboda matsalar tsaro

Makarantun kwana za su koma ranar 16 ga Mayu, 2021.

Gwamnatin Kano ta ba da umarnin bude makarantun kwanan da ta rufe a farkon shekarar nan a jihar saboda matsalar tsaro.

Hakan na kunshe ne a cikin umarnin da ta bayar komawa makarantu a ranar Litinin 17 ga Mayun 2021, bayan kammala hutun Karamar Sallah.

Kwamishinan Ilimin Jihar, Muhammad Sanusi-Kiru, ta hannun kakakin Ma’aikatar, Aliyu Yusif, ya ce “Ana umartar daliban makarantun kwana su koma makaranta a ranar 16 ga Mayu, 2021, makarantun je-ka-ka-dawo kuma 17 ga Mayu, 2021.

“Gwamnati na kokarin tabbatar da ganin yara sun samu ingantaccen ilimi; don haka ana bukatar iyaye da su mayar da ’ya’yansu makarantu a kan lokaci,” inji sanarwar.