✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kano: Daliban JSS1 da SS1 sun koma makaranta

Kwamishinan ilimin jihar Muhammad Sunusi Kiru ne, ya bayyanawa cewa daliban su koma ranar 16 ga watan Nuwamba.

A yau ne daliban aji daya (JSS1) na karamar sakanda da babbar sakandare (SS1) suka koma makaranta a jihar Kano.

Kwamishinan Iliminjihar, Muhammad Sanusi Kiru, ya sanar da hakan a sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na ma’aikatar Aliyu Yusuf fitar.

“Ya kamata daliban makarantun Firamare 1-6 su sake komawa gaba daya daga ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, sabanin umarnin farko da aka sanya musu ranakun zuwa makaranta”, inji shi.

Ya yi kira ga iyayen da yaransu ke wadannan azuzuwan da su yi biyayya ta hanyar dawo da su a ranakun da aka sanya.

Daga nan sai kwamishinan ya umarci daraktoci da shugabannin makarantu da sauran masu ruwa da tsaki da su kasance cikin shiri don ci gaba da aikin.

Idan ba a manta ba, gwamnatin jihar ta umurci daliban JSS-1 da SS-1 da su kasance a gida na tsawon makonni biyar domin an kammala jarabawar masu kammala karama da babbar sakandare.