Daily Trust Aminiya - Kano: Shugaban Karamar Hukuma ya nada mataimaka 55

Hassan Garban Kauye Farawa, Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso, Jihar Kano

Kano: Shugaban Karamar Hukuma ya nada mataimaka 55

Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano, Hassan Garban Kauye Farawa, ya nada masu taimaka masa na musamman gauda 55.

Hassan Garban Kauye Farawa, ya ce hadaman na musamman za su taimaka masa wurin gudanar da harkokin Karamar Hukumar.

“Nadin hadimai 55 sakamako ne na kokarin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kawar da talauci a tsakanin matasa da kuma farfado da tallain arziki musamman a lokacin da ake cikin matsala,” inji shi.

Don haka ya yi kira gare su da su nuna kishi da sadaukar da kai wajen ciyar da Karamar Hukumar gaba tare da kare mutuncinta.

Nade-naden na zuwa ne bayan tun da farko, Kansilan Gundumar Gurungawa a Karamar Hukumar ya nada hadimai 18, lamarin da ya ja hankalin jama’a.

Kansilna ya kuma sadaukar da albashinsa na farko domin tallafa wa nakasassu 100 a gundumarsa.

Karin Labarai