✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kano ta ba da aikin hanyar miliyan N500 a biliyan N1.4

Gwamnatin Kano ta kwace aikin titin Ahmadu Bello bisa zargin dan kwangila da jan kafa

Gwamnatin Jihar Kano ta soke aikin gyaran hanyar ta da bayar bisa zargin dan kwangilar da jan kafa wurin kammalawa.

Bayan kwace aikin da aka bayar a kan Naira miliyan 500 gwamnatin ta sake bayar da shi ga wani kamfani na daban a kan Naira biliyan 1 da miliyan 400.

Yanzu kamfanin Traiacta Nigeria Limited ne zai aiwatar da kwangilar da aka kwace daga Tiamin Multi-Services Global Limited.

Aminiya ta ruwaito cewa an jima ana kai komo tsakanin gwamnatin jihar da Tiamin Multi-Services Global Limited wanda gwamnatin ke zargi da hannu a bullar bidiyon zargin Gwamna Abdullahi Ganduje karbar rashawar dololi.

Da yake jawabi bayan taron Majalisar Zartarwar Jihar, Kwamishinan Watsa Labarai, Muhammad Garba ya ce tuni aka ba wa sabon dan kwangilar kashi 15 na kudin aikin, wanda ya kai miliyan N84.6 kuma aikin da aka kammala ya kai kashi 12.

Ya ce aikin ya kunshi ginin magudananan ruwa da kwalbatoci da duk abin da ya danganci aikin.