✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano ta fara shirin zaben kananan hukumomi

Hukumar Zabe ta Jihar Kano (KANSIEC) ta ce tuni ta fara shirye-shiryen gudanar da zabukan kananan hukumomi da ta tsara gudanarwa a shekara ta 2021.…

Hukumar Zabe ta Jihar Kano (KANSIEC) ta ce tuni ta fara shirye-shiryen gudanar da zabukan kananan hukumomi da ta tsara gudanarwa a shekara ta 2021.

Shugaban hukumar, Farfesa Garba Ibrahim Sheka ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, yayin da ya karbi bakuncin ’yan kwamitin zartarwa na hadakar jam’iyyu (IPAC) a ofishin hukumar.

Ya kuma ba su tabbacin yin aiki tare da dukkan jam’iyyun ba tare da nuna bambanci ba, kuma sun shirya tsaf domin ganin cewa ba a sake samun matsalar rashin kai kayan zabe a kan lokaci kamar yadda aka fuskanta ba a zaben 2018.

Sheka a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Dahiru Lawan Wambai ya fitar ya ce tuni shirye-shirye suka yi nisa wajen ganin an gudanar da zaben ba tare da tangarda ba.

A nasa jawabin, shugaban IPAC, Isa Nuhu Isa ya tabbatar wa KANSIEC ci gaba da bayar da hadin kai da goyon baya domin a samu sahihin zabe.

Idan za a iya tunawa, tun a watan Yulin da ya gabata Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin sauya fasalin shugabancin Jam’iyyar APC a Kananan Hukumomi 44 na Jihar a shirye-shiryen zaben da ke tafe.

Kakakinsa Abba Anwar a wata sanarwa a baya ya ce an kafa kwamitocin sasanta ’yan jam’iyyar da zai zagaya kowace mazaba a jihar domin kara karfafa jam’iyyar.