✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kansila ya nada mataimaka 18 a Kano

Ranar Alhamis ake kaddamar da hadiman a Sakatariyar Karamar Hukumar Kumbotso.

Kansilan Mazabar Guringawa a Karamar Kukumar Kumbotso ta Jihar Kano ya nada hadimai 18 da za su mataimaka masa wurin gudanar da harkokin yankin.

A wasikar nadin hadiman da Aminiya ta gani, Kansilan Guringawa, Muslihu Yusuf Ali ya ce za su taimaka masa ne wajen sauke nauyin da ke kansa a wasu fannoni na tabbatar da cigaban yankin.

“Ina sanar da jama’a nadin mataimakan da za su taimaka min wajen sauke nauyin da ke wuyana a fannoni daban-daban na tabbatar da ci gaba, walwala, tsaro da kuma jin dadin al’ummar Guringawa,” inji sanarwar.

Aminiya ta gano cewa a ranar Alhamis 11 ga watan Maris, 2021 ake kaddamar da hadiman a Sakatariyar Karamar Hukumar Kumbotso.

Daga cikin wadanda aka nada akwai: 

  1. Sulaiman Ibrahim Bako, Mataimaki na Musamman
  2. Yahaya Abdu Yahaya, Babban Sakatare na Musamman
  3. Kamalu Garba LY, Kafafen Watsa Labarai na Zamani 
  4. Usama Umar Zubair, Mashawarci na Musamman kan Harkokin Addini.

Sauran mukaman su ne:

  • Mashawarci kan Tallafi da Harkokin Jinkai 
  • Mashawarci kan Kafafen Sa Da Zumunta
  • Mashawarci kan Kungiyoyi Masu Zaman Kansu da Zuba Jari 
  • Da kuma Mashawarci kan Harkokin Siyasa da sauransu.