✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kansiloli sun dakatar da ciyaman kan badakalar N40m

Ana zargin ciyaman din da ruf da ciki kan kudin wani makeken fili.

Kansiloli a Karamar Hukumar Tafa a Jihar Neja sun dakatar da Shugaban Karamar Hukumar, Ibrahim Mami Ijah, kan zargin badakalar sayar da fili.

Kwafin takardar dakatarwar da Aminiya ta gani, kansiloli 10 ne suka rattaba hannu suna zargin ya sayar da wani fili da ke bayan tsaunin Zuma Rock, da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a kan Naira miliyan 40.

Kansilolin sun ce sayar da filin da ciyaman din ya yi karan tsaye ne ga dokokin kananan hukumomi.

Sun kuma zarge shi da yin almubazzaranci tare da karkatar da kudaden gudanar da ayyuka, musamman ma aikin gina hanyoyin da ake yi a Ijah da Ijah-Koro, da New Bwari da New Wuse da ma aikin gina gidan bakin karamar hukumar da ke kan hanyar Garam.

Sun kuma zarge shi da gaza yin cikakken bayani kan kudaden harajin da karamar hukumar ta samu. 

Duk kiran wayarsa da ma aika masa rubutaccen sako da Aminiya ta yi, Shugaban Karamar Hukumar da aka dakatar din ya ki cewa uffan game da dakatarwar.