✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kar a manta da talakawa a lokacin Azumi — Buhari

Ina kira ga Musulmi a Najeriya da su dabi’antu da halayya ta hakuri da juriya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi lale maraba da shigowar watan Azumin Ramalana, inda yake kira ga al’ummar Musulmi a kan kada su manta da halin da talakawa ke ciki da kuma ’yan gudun hijira a wannan wata mai tarin falala.

Hakan na kunshi ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu ya fitar yayin zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a yammacin Litinin.

Buhari cikin sakonsa na taya musulmai murnar fara Azumin Ramadana, ya yi addu’ar Allah ya karbi ibadu sannan kuma ya hada kan al’ummar kasar nan tare da azurta ta da zaman lafiya da kuma aminci.

Sanarwar ta ce Buhari yana kira ga Musulmi a Najeriya da su dabi’antu da halayya ta hakuri da juriya sannan su kau da idanu da toshe kunnuwa a kan muryoyin da ke kira zuwa ga rabuwar kai a kasar nan.

Kazalika, shugaba Buhari ya kuma bukaci ’yan kasar da su tausaya wa talakawa da nuna jin kai a garesu, tare da neman a rika tunawa da wadanda rikici ya raba da muhallansu ta hanyar sanya su cikin addu’o’i da kyautata musu a wannan lokaci na azumi.

A ranar Talata ce Musulmi a wasu kasashen duniya ciki har da Najeriya suka tashi da Azumi bayan ganin jinjirin watan Ramadana a yammacin Litinin.