✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kar INEC ta bari PDP da dagula Zaben 2023 —APC

Take-taken PDP shi ne ta ci zaben gwamnan Jihar Zamfara ko ta halin kaka.

Jam’iyyar APC mai mulki ta gargadi Hukumar Zabe ta kasa INEC cewa, kar ta kuskura ta kyale jam’iyyar PDP ta dagula lamura a zaben da za a yi na shekarar 2023.

Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa shiyar Arewa maso Yamma, Salihu Mohammed ne ya yi wannan gargadin a cikin wani furuci da ya yi a Abuja a ranar Talata.

Mataimakin shugaban ya furta hakan ne bayan da wata Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau ta yanke hukunci watsi da nasarar dan takarar gwamnan Jihar Zamfara na jam’iyyar PDP.

“Yanzu dai PDP ba ta dan takarar gwamna a zaben 11 ga watan Maris na shekarar 2023…. umarnin kotu shi ne PDP ta je ta yi halastaccen zaben fitar da gwani karkashin kulawar INEC,” a cewar Salihu Mohammed.

Ya ce, take-taken PDP shi ne ta ci zaben gwamnan Jihar Zamfara ko ta halin kaka, “domin jam’iyyar da ta kasa yin halarci a cikin gida, babu yadda za ta yi halarci a zabe na jama’a.”

Kazalika, ya yi kira ga duk ‘yan takarkaru a kowanne mataki da su tsaya tsayin daka don ganin cewa PDP ba ta yi magudin zabe ba don gudun kakaba wa jama’a wanda bai ci zabe ba a jihar.