✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kar sojoji su kuskura a hana zaben gwamnan Anambra —Buhari

Buhari ya umarci jami'an tsaro su dauki duk matakan da suka dace a yi zaben.

Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci sojoji da sauran hukumomin tsaro su tabbata babu abin da ya hana gudanar da zaben gwamnan Jihar Anambra da aka shirya gudanarwa ranar 6 ga watan Nuwamba mai kamawa.

Mai ba shi shawara kan tsaro, Babagana Monguno, ne ya sanar da umarnin, lura da karuwar matsalar tsaro a yankin Kudu maso Gabas, sakamakon hare-haren ta’addancin haramtacciyar kungyar IPOB.

“Buhari ya ba da umarni cewa, babu dalilin a bari wani abu ya hana gudanar da zaben cikin nasara. Mutane na da ’yancin jefa kuri’a su zabi shugabanninsu.

“Babu wani mutum ko kungiya da za a bari su haddasa yamutsi ko kashe-kashe.

“Shugaban Kasa ya fada wa sojoji da sauran hukumomin tsaro karara cewa su dauki duk matakan tabbatar da ganin an gudanar da zaben, ko da kuwa ta hanyar mamaye wuraren ne da jami’an tsaro.

“Akwai illoli da dama a bari masu tayar da kayar baya su hana gudanar da zabe; farko dai tsarin dimokuradiyya muke bi, na biyu kuma idan aka bari bata-garin suka hana gudanar da zabe, to wasu ma za su bi sahunsu a wasu sasssan kasar nan,” inji Monguno.

Shi ma a jawabinsa kan zaben na Anambra, Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Maigari Dingyadi, ya ce a shirye ’yan sanda suke su tabbatar da tsaro a Jihar Anambra da ma sauran sassan Najeriya.

“Mun tattauna musamman a kan zaben gwamnan Jihar Anambra da za a yi ranar 6 ga Nuwamba, 2021, kuma ina ba wa jama’ar jihar Anambra da daukacin ’yan Najeriya tabbacin gwamnati na gudanar da zaben.

“Dole zaben ya kasance sahihi kuma za su yi duk abin da ya dace domin tabbatar da ganin cewa an samar da isasshen tsaro. Wannan shi ne kadai hanyar kare tsarin dimokuradiyya da kuma tabbatar da shugabanci nagari,” inji shi.