✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Karamar Sallah: An jibge jami’an tsaro 3,000 a Kano

Kwamanda Idris Adamu ya yi kira ga al'umma da su ba su hadin kai a lokacin bukukuwan Sallar

A yunkurinta na samar da tsaro ga al’umma yayin bikin Karamar Sallar bana, rundunar tsaro ta farin kaya reshen Jihar Kano, ta tanadi jami’ai 3,028 da za su yi sintiri a masallatai da manyan shaguna.

Kwamandan rundunar, Idris Adamu Zakari ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce an zakulo wadannan jami’ai ne daga sassa daban-daban na rundunar.

“Za mu fi maida hankali kan wuraren da dukiyar gwamnati take, hadi da filayen Sallar Idi da kuma manyan shaguna,” in ji kakakin rundunar, DSC Ibrahim Idris Abdullahi a sanarwar.

A don haka ya yi kira ga jami’an da su tabbatar tsaron ya samu a lokacin bukukuwan Sallar, tare da kira ga al’ummar Kano da su ba da hadin kai wajen ganin an samu abin da ake so.

Idris Adamu ya kuma yi wa al’ummar Musulmi fatan za su gudanar da bukuwan Sallah lafiya, tare da kai rahoton duk wani motsi da ba su gamsu da shi ba ga cibiyar tsaro mafi kusa da su.