✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karamar Sallah: ‘Ba za a ga wata ranar Talata ba’

Dan kwamitin ganin wata ya ce ko a ranar Laraba, ba za a ga watan cikin sauki ba.

Ganin watan sabon watan Shawwal na Karamar Sallah zai yi wuyar gani a ranar Talata 29 ga watan Ramadan 1442 Hijiriyya.

Wani dan Kwamitin Ganin Wata na Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Simwal Usman Jibril, ne ya bayya hakan a yayin da Musulmin Najeriya da wasu kasashe ke fara duban watan Shawwal a yammacin Talata gabanin Karamar Sallah.

“A ranar Talata, ranar da muka kai azumi 29 a lokacin da rana za ta fadi a Najeriya, ba a ma riga an haifi watan ba. Ko an fita neman watan ba za a iya ganin sa ba saboda babu watan a sama,” inji Masanin Taurarin.

Tuni dai umarnin duba sabon watan ya fito daga Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban NSCIA, kasancewar Talatar ita ce 29 ga Ramadan 1442 Hijiriyya.

Watan Ramadan da sauran watannin Musulunci na da kwana 29, amma idan ba a ga jinjirin wata ba a ranar, ana cikawa zuwa kwana 30.

Simwal ya yi bayani cewa hasashe ya nuna sabon watan Shawwal zai bullo ne dab da Sallar Isha a ranar Talata, saboda haka zai yi wuya a iya ganin sa kafin faduwar rana.

Hakan na nufin lokacin da rana za ta fadi, wanda shi ne lokacin duban wata, ba a riga an haifi sabon watan Shawwal ba.

“Kasancewa sai karfe 8 na dare [na nufin], to ba za a samu tsayuwar sabon watan ba ke nan sai bayan an kai karshen azumin ranar 29.

“Wannan yana nuna cewa bayan Magariba, lokacin da za a nemi sabon watan, ba a ma haife shi ba, ballanta a iya ganin shi a Najeriya da sauran kasashe na duniya.

“Amma washegari, ranar Laraba 12 ga watan Mayu a Najeriya, sabon watan zai kasance sama da awa 22 da haihuwa… Ganin shi da na’urar hangen nesa zai yiwu cikin sauki.

“Amma ganin sa da ido sai idan gari ya kasance wasai kuma mai neman watan yana da kwarewa, [shi ne] zai iya ganin sa cikin sauki.

“Wannan ke nuna abin da zai sa ganin sa a ranar 30 din ma shi ne saboda haihuwarsa da aka yi a cikin daren ranar da ta wuce.

“Shi ya sa ba za a gan shi da sauki a sama ba kamar yawancin ranakun 30 ga wata ba, inda [wata] yake tsayawa har bayan Sallar isha; amma wannan kusan minti 41 zai yi a sama,” inji shi.