✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karancin abinci na kara tsananta a Arewa maso Gabas – MDD

Karancin abinci na kara tsananta a Arewa maso Gabas - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta koka kan yadda ta ce rikicin Boko Haram ya mayar da mata masu yawa marasa galihu musamman ta bangaren karancin abinci a yankin Arewa maso Gabas.

Babban Jami’in Majalisar a Najeriya kuma mai kula da ayyukan jinkai, Matthias Schhmale, ne ya bayyana haka, inda ya ce rikicin ya fi kamari musamman ga marasa galihu da kananan yara.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci sansanin El-Miskin da ke Maiduguri a Jihar Borno.

Yayin ziyarar, jami’in ya ce ya tarar da kimanin ’yan gudun hijira 7,200 da suka nemi mafaka a wajen.

A cewarsa, yanayin abinci ya yi tsanani ga iyalai da dama a sansanin saboda rashin kudaden gudanar da ayyuka.

Ya ce, “Mata sun shaida min cewa sama da wata iuku ba su samu tallafin abinci ba, kuma suna kokawa da yadda za su ciyar da iyalansu, wasu yaran sun bayyana cewa sun shafe kwanaki da yawa ba tare da sun ci abinci sosai ba, iyaye mata suna gaya mini cewa ’ya’yansu na kwana suna kuka saboda yunwa.

“Haka nan a cikin shirin ciyar da marasa lafiya na Majalisar ta Dinkin Duniya su ma suna gaya min cewa sun riga sun ga an shigar da yara da dama asibiti da ke da matsananciyar jinyar rashin abinci mai gina jiki, wannan abin damuwa ne,” a cewarsa.

Ya ce mutanen da ya gana da su a sansanin na El-Miskin na daga cikin kimanin mutane miliyan 4.4 da za su bukaci tallafin abinci na gaggawa a bana.

Ya ce mutanen galibi sun fito ne daga jihohin Adamawa da Borno da Yobe, kamar yadda binciken wata cibiya mai suna Cadre Harmonisé na watan Oktoba 2022 ke nunawa.