✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Karancin kudi da wahalar fetur sun haifar da zanga-zanga a Ibadan

'....mun yi zanga-zanga ne don nuna adawa da zaluncin Gwamnan CBN'

Wasu mazauna Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, sun gudanar da zanga-zanga a wasu manyan titunan birnin a ranar Litinin don nuna rashin jin dadinsu dangane da matsalar mai da karancin takardun kudin da suke fuskanta.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa, da fari, masu zanga-zangar sun hadu ne a babbar kofar shiga Jami’ar Ibadan kafin daga bisani suka hau manyan hanyoyin yankin.

Bayanai sun nuna an girke jami’an tsaro da dama kuma a wurare daban-daban don hana yi wa doka karan tsaye.

Masu zanga-zangar wanda galibinsu masu rajin kare hakkin dan Adam ne, sun ce sun dauki wannan mataki ne saboda jefa ‘yan Najeriya cikin matsin da ba su yi zato ba.

Daya daga cikin jagororin zanga-zangar, Solomon Emiola, ya ce sun yanke shawarar yin zanga-zanga ne domin ‘yan Najeriya su nuna wa duniya rashin jin dadinsu game da halin da aka je fa su.

“Mun fito ne a matsayinmu na ’yan Najeriya don mu nuna rashin yardarmu da zaluncin Gwamnan CBN.

“Makonni ke nan ‘yan Najeriya na kuka wasu na mutuwa saboda rashin samun zarafin cire kudaden da suka tara da zufansu a bankuna.

“Da karancin kudin da ake fama da shi ba za mu iya sayen mai a kan N350 da N400 lita guda ba,” in ji Emiola.

(NAN)