✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Karawa sarakuna albashi a Gombe abu ne da aka dade ana jira’

Ya ce matakin cika alkawarin da Gwamnan ya dauka ne lokacin yakin neman zabe.

Tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban Kasa kuma Kwamishinan Lafiya na farko a Jihar Gombe, Dokta Ibrahim Jalo Daudu, ya ce karawa sarakuna albashi da gwamnatin Jihar ta yi abin yabo ne.

Ya bayyana hakan a zantawar sa da Aminiya a Gombe, inda ya ce an jima ana jiran wannan rana da za a daga martaba da kimar sarakuna a Jihar.

A cewarsa, “Ba a mutunta su a da, kuma ba wata kulawa da ake basu, amma duk abin da ya faru su ake fara saka wa a gaba su yi magana.”

Ya ce duk da dai karain albashin alkawarin da Gwamna ya dauka ne lokacin yakin neman zabe ya kamata a yaba masa.

Dokta Ibrahim ya kara da cewa yanayin da ake ciki na rashin tsaro a kasar nan, sarakuna sune a kan gaba wajen yi wa mabiyan su gargadi kan kaucewa shiga ayyukan ta’addanci amma kuma ba a kula da su.

Dagan an sai ya hori sarakunan da su hada kai da gwamnati wajen kare yankunan su daga barazanar tsaro, suna kuma kai rahoton dukn wa I abin da ba su amince da shi ba ga mahukunta.

Ya kuma roki a shigar da sarakunan cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya don a rika damawa da su saboda suna da rawar takawa.

Tsohon Kwamishinan ya kuma jinjina wa Gwamna Inuwa Yahaya, bisa karin da ya yi, har ma da alkawarin gina musu gidaje.

Ya kuma roki al’ummar Jihar da su zama masu biyayya ga gwamnati dan ba ta dama ta ci gaba da ayyukan raya kasa.