✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kare mafi arziki a duniya zai sayar da gidansa kan sama da N13bn

An kiyasta darajar gidan a kan makudan kudi da suka kai Dalar Amurka miliyan 32.

Wani kare mai suna Gunther VI, wanda ya gaji dukiyarsa da ta samo asali daga wata Bajamushiya marigayiya Countess Karlotta Leibenstein, wadda tsohuwar mawakiya ce, kuma yake kwana a cikin dakin mamallakiyarsa wanda ya zama kare mafi arziki a duniya ya sa gidansa a kasuwa!

Gunther VI, wanda ya mallaki Dalar Amurka miliyan 500 (kimanin Naira biliyan 204 da miliyan 945) ta hanyar gado, yana shirin sayar da katafaren gidan nasa na alfarma ne da ya gada daga kakansa wani kare da ake kira Gunther III, wanda shi kuma ya gaji dimbin dukiyar daga mamallakiyarsa, KarlottaLiebenstein, wacce ta mutu a 1992.

Daga cikin dukiyar da karen ya gada akwai wani babban gini Tuscan a Italiya, wanda karen yake rayuwa a ciki.

Gunther VI ya mallakikatafaren gida mai daki tara da dakin wanka takwas da rabi da Madonna ta taba mamayewa a rukunin gidaje na Miami.

Wani bangaren gidan da kare Gunther VI ya gada da zai sayar

Gidan wanda yake bakin ruwa an mika shi ga Gunther VI a matsayin gadonsa, kuma an kiyasta shi a kan makudan kudi da suka kai Dalar Amurka miliyan 32, (wanda ya kai Naira biliya 13 da miliyan 154 da dubu 560).

Dukiyar karen ta fito ne bayan rasuwar mamallakiyar karen Karlotta Leibenstein a 1992 wadda ta bar wasiyyar dukiyoyinta na kimanin Dala miliyan 80 (kimanin Naira biliyan 330 da dubu 962 da 480 ga Gunther III – kakan Gunter VI – saboda ba ta da ko ’ya’ya ko dangi na kusa, a cewar wasu rahotanni.

Mutanen da ke kula da karen sun tara kimanin Dala miliyan 500 (Naira biliyan 204 da miliyan 945) kuma sun zuba kudin Gunther a wasu gidaje a kasashe da dama.

Lokacin da ya zo sayar da babban gidansa na Miami, Gunther ya ba dillaliyar gidaje Ruthie Assouline da Kungiyar Assouline a Compass, don daukar ragamar kula da dukiyar.

“Mun sayar da gidaje na miliyoyin daloli amma babu shakka wannan ne na farko,” kamar yadda Ruthie ta bayyana wa mujallar PEOPLE.

“Lokacin da masu kula da su suka gaya mani cewa kare ne ya mallaki kadarorin, ban yarda ba.”

Ruthie, wacce take hadin gwiwa da Ethan Assouline, dole ta yi gwajin numfashi kafin ta samu izini daga Gunther ta hanyar haushi.

“A ganawarmu ta farko da Gunther, ya ruga zuwa gare ni, ya yi mini wata babbar sumbata kuma ya share min jambaki.

“Ina tsammanin wannan shi ne ainihin abin da ya rufe yarjejeniyar!”

Gidajen karen suna wani yanki mai fadin murabba’in kafa 51,000, kimanin kafa 100 a gaban wani ruwa.

Yana da fasalin shimfidar wuri mai fadi da budadden ruwa da fuskar hanyar shiga birni da tafki, akwai wurin ninkaya, inda Gunther ke shiga ya jika jikinsa da rana, lokacin ziyartar Miami daga Italiya, inda yake zaune dindindin.