✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kare ya kashe yaro dan shekara 10 a Ingila

’Yan sandan yankin sun ce jami’ai sun hallaka karen.

’Yan sanda sun ce wani kare ya kashe wani yaro dan shekara 10 a unguwar Lorrine Urvine da ke Ingila a Birtaniya.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito faruwar lamarin a wani gida da ke unguwarsu da misalin karfe 4 na yamma a ranar Litinin.

Ma’aikatan lafiya sun ruga wajen da lamarin ya faru inda suka tabbatar da mutuwar yaron.

’Yan sandan yankin sun ce jami’ai sun hallaka karen kuma za su ci gaba da zama a yankin yayin da ake gudanar da bincike.

Wani mazaunin unguwar ya ce abin ya faru ne a daya daga cikin gidajen da ke kan layin, lamarin da ya ce ya razana shi.

Shi ma wani dan unguwar Lorrine Urvine ya ce, “Ba abin da muke iya gani sai ihu da muka ji. Yaron sun razana sosai.

“Mintuna kadan da faruwar lamarin na ga motocin ’yan sanda masu yawan da ban taba ganin irinsu ba a rayuwata.”

Makwabcin ya ce “Wani yaro ya ruga wani gida yana ce musu ga kare ya kai wa abokinsa hari amma makwabcin ya kasa yin komai don ceton yaron.”

Mahaifiyar yaron ta ce ta ji matukar takaicin mutuwar danta.

A shafinta na Facebook ta ce “karen ba na gidanmu ba ne, kuma ba a gidanmu abin ya faru ba.

“Dana Jack Lis ya fita ne don yin wasa. Mun yi kewarka sosai danmu, abin kaunarmu.”

Har yanzu ’yan sanda ba su iya gano wane irin nau’in kare ne ya kai harin ba.