Karin albashi karin talauci ne ga ’yan Najeriya | Aminiya

Karin albashi karin talauci ne ga ’yan Najeriya

Muna godiya gare ku tare da fatar alheri mai yawa. Muna so ku isar mana da kukanmu ga Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago a kan matsalar karin albashin  ma’aikata a Najeriya. Neman karin albashi ko tafiya yajin aiki matsala ce ga talakawa tun farko. Duk lokacin da aka yi karin albashi wasu kamfanoni da azzaluman ’yan kasuwa sai su kara farashin kaya ga ma’aikata da wanda ba ya da albashin. Abin da za su yi shi ne, su nemi gwamnati ta daidaita farashi. Kowa ya saya da arha. Amma su sani karin albashi, karin yawan matalauta ne.Tsarin gwamnati na rage talauci zai yi wuya.

 

Daga Suleiman Adam KFD, Auyo Jigawa. 07017846306.