✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Karin Albashi: Ma’aikata sun tsunduma yajin aiki a Afirka ta Kudu

Gwamnati ta dage a kan karin kashi 3%.

Dubban ma’aikata ne suka tsunduma yajin aiki a fadin Afirka ta Kudu a kokarin ganin an yi masu karin albashi da kuma inganta walwalar yanayin aiki.

Kafafen yadda labaru na cikin gida na cewa wannan ne karo na farko da ma’aikatan gwamnati na kasar suka shiga irin wannan yajin aikin a cikin shekara goma.

Ana sa ran yajin aikin zai kawo cikas ga tafiyar da lamurra a ma’aikatun gwamnati da filayen jirgin sama.

Fara yajin aikin ya biyo bayan kasa cimma matsaya tsakanin Kungiyar Kwadago ta kasar da bangaren gwamnati.

Kungiyar na bukatar a yi wa ma’aikata karin albashi na kashi 7%, yayin da gwamnati ta dage a kan karin kashi 3%.