Daily Trust Aminiya - Karin dalibai biyar na Kwalejin Noma ta Kaduna sun kubuta
Subscribe

Kwalejin Horar d Harkokin Noma da Gandun Daji

Karin dalibai biyar na Kwalejin Noma ta Kaduna sun kubuta

’Yan daban daji sun sake sako karin wasu dalibai biyar na Kwalejin Harkokin Noma da Gandun Daji ta Kaduna, wadanda aka yi garkuwa da su tun a watan Maris.

Haka na zuwa ne bayan kwanaki uku da wasu dalibai biyar na Kwalejin suka kubuta daga cikin 39 da aka sace a garin Afaka.

Aminiya ta ruwaito cewa, a halin yanzu daliban biyar da suka kubuta suna kan hanyarsu ta zuwa asibiti domin a tabbatar da ingancin lafiyarsu.

Ya zuwa yanzu, dalibai goma ne suka kubuta, a yayin da 29 ke ci gaba da zaman zulumi a hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

More Stories