✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin haraji ya sa direbobin manyan motoci zanga-zanga a Bayelsa

Karin harajin ya janyo direbobin rufe wasu manyan hanyoyin shiga babban birnin jihar.

Direbobin manyan motoci da dillalai sun shiga zanga-zanga kan karin haraji da gwamnatin jihar Bayelsa ta ke musu.

Direbobin sun tare hanyar shiga babban birnin jihar a kofar shiga ta Igbogene a safiyar ranar Talata tare da dakile zirga-zirga a ciki da wajen jihar.

Da yake magana da ‘yan jarida a wurin zanga-zangar, shugaban kungiyar direbobin a jihar, Mista Ikechukwu Nweke, ya ce kafin matsalar ta fara a ranar Litinin su kan biya N7,000 a kullum.

Sai dai ya ce tun bayan lokacin ne ma’aikatan gwamnati suka hana manyan motocin da ke dauke da kayan shigowa jihar sai sun biya karin N2000 daga N7000 din da suke biya kullum.

Ya ce “Mun kasance muna biyan N7000 akan kowace mota kullum, domin karbar haraji, duk da cewa kudin ya wuce gona da iri.

“Amma a matsayinmu na mutane masu son zaman lafiya, muna ba su hadin kai. Kwatsam sai a ranar Litinin suka hana manyan motocinmu daukar kayan cikin jihar sai da aka musu karin N2000 wanda ya kai N9000 a yanzu.

“Gwamnati ta bullo da hadadden haraji, mun bi ka’ida, don kawai mu gudanar da kasuwanci cikin kwanciyar hankali a nan jihar Bayelsa, amma ofishin kula da tsaftar muhalli ya sake fito da wani karin kudin, a ina muke da kudin da za mu biya dukkan wadancan harajin.

“A baya muna biyan 6,000, sannan ga 1,000 na tikiti, sai kuma gashi hukumar tsaftar muhalli ta fito da wani sabon harajin, duk da cewar mun aike wa da gwamnatin kokenmu amma ba abin da ya sauya,” in ji shi.

Wakilin kudaden shiga na gwamnatin jihar, Mista Doubra Kumokou, ya ce gwamnatin da ta gabata ta bullo da tsarin haraji na bai daya don takaita yawan harajin.

Sai dai ya ce ya yi mamaki matuka lokacin da Ofishin Kula da Tsaftar Muhalli ya bullo da karin haraji ba tare da ko da tuntubar wakilin harajin ba.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta shiga tsakani ta sasanta lamarin cikin ruwan sanyi.

Kwamishiniyar Sufuri ta Jihar, Misis Grace Ekiotene, ta ce ma’aikatar za ta gana da dukkan kungiyoyin kwadagon don magance matsalar.