✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin jihohin Amurka 4 sun haramta zubar da ciki

Wasu karin jihohin Amurka hudu da ’yan Jam’iyyar Republican ke jagoranta za su haramta zubar da ciki a wannan makon. Matakin nasu na zuwa ne…

Wasu karin jihohin Amurka hudu da ’yan Jam’iyyar Republican ke jagoranta za su haramta zubar da ciki a wannan makon.

Matakin nasu na zuwa ne yayin da wasu gungun dokokin da suka takaita tsarin suka fara aiki bayan hukuncin da Kotun Kolin kasar ta yanke na soke shi.

Ya zuwa yanzu, jihohi 13 sun zartar da hukuncin haramta zubar da ciki bayan kotun ta yi watsi da ikon da Kundin Tsarin Mulkin kasar ya ba Gwamnatin Tarayya a kai na kawo karshen zubar da cikin.

Yawancin wadancan jihohin dai sun fara aiwatar da haramcin zubar da cikin jim kadan bayan yanke shawarar yin hakan a ranar 24 ga Yuni.

Amma jihohin Idaho da Tennessee da Texas sun jira kwanaki 30 bayan da aka shigar da kudurin dokar domin zartarwa, wanda ya fara makonni bayan an sanar da hukuncin.

Wannan wa’adin ya cika ranar Alhamis.

Duk wadannan jihohin ban da North Dakota sun riga sun sami dokokin hana zubar da cikin, in ban da a wadanda rashin lafiya ta tilasta musu bukatar zubarwar.

Kuma galibin asibitocin da ke ba da damar zubar da ciki a yankunan ko dai sun daina ba da wadannan damar ko kuma su koma wasu jihohin da suka amince da shi.

Jihar Texas, ce ta biyu mafi girma a kasar, ta haramta yawancin zubar da ciki da zarar an gano ana shirin yin hakan, wanda zai iya kasancewa a makonni shida na farkon samun juna biyu kafin mata da yawa su san suna da ciki.

An shafe kusan shekara guda ana yin wannan haramcin tun bayan da kotuna suka ki dakatar da dokar a watan Satumban bara.