✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin kasafin N895bn: Majalisa ta kammala karatun farko

Ta mika karamin kasafin ga Kwamitin Rabon Kudade domin kawo rahoton.

Majalisar Dattawa ta kammala karatun farko kan karin kasafin Naira biliyan 895 da Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya gabatar mata.

Majalisar ta amince da yin karatu na biyu kan karin kasafin ne bayan muhawara da mambobi suka yi a kai.

Hakan ta faru ne washegarin da Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan ya karanta bukatar Shugaban Kasar na neman amincewar Majalisar.

Buhari ya gabatar da karamin kasafin ne domin samun kudaden sayo karin makaman sojoji da kuma allurar rigakafin cutar COVID-19.

Bayan karatu na biyu a kan kasafin, Shugaban Majalisar ya mika wa Kwamitin Rabon Kudade, domin ya kawo rahoto a ranar Talata mai zuwa.

Karin kasafin ya kunshi Naira biliyan 722.4 domin sayen makamai, ragowar kuma domin yaki da cutar COVID-19.