✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin kudin kiran waya: An sa zare tsakanin Gwamnati da kamfanoni

Kamfanonin sadarwa sun ce karin kudin kiran waya zuwa N53 ya zama dole, gwamnati ta ce allambaran

Gwamnatin Tarayya na kai ruwa rana tsakaninta da kamfanonin sadarwa kan shirinsu na kara kudin kiran waya da na data.

Cikin wasikar da ta aika wa Hukumar Sadarwa ta Najeiya (NCC), Kungiyar Kamfanonin Sadarwa ta Najeriya (ALTON) na shirin kara kudin kira da na rubutaccen sako da kashi 40 cikin 100.

Kamfanonin sun ce, daukar wannan mataki ya zame musu dole duba da yadda suke fuskantar tsadar gudanar da harkokinsu a kasar.

Don haka za su kara kuidn kiran waya zuwa N53.7 minti guda, rubutaccen sako kuma daga N4 zuwa N5.6, sannan gigabait daya na data zai koma N3,200.

ALTON ta ce kamfanonin sadarwar suna fuskantar kalubale sosai a Najeriya tun bayan bullar annobar COVID-19 a 2020 da kuma yakin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine.

Kungiyar ta ce yakin Rasha da Ukraine ya sa kamfanonin fuskantar karin farashin man gas da suke amfani da shi da kashi 35 cikin 100.

Haka nan, ta ce karin haraji da kashi biyar da aka yi musu a Najeriya na daga cikin abubuwan da suka kara wa kamfanonin nauyin da ke kansu na harajin da suke biya.

Wasikar, mai dauke da sa hannun Shugaban ALTON, Injiniya Gbenga Adebayo, ta nuna cewa, “Da wannan dalili ne ALTON take ganin ya dace kamfanonin sadarwar su rika waiwayen farashinsu domin rage radadin kalubalen tattalin arziki da mambobinmu ke fuskanta.

“Duba da halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki, muna neman kara kudin kiran waya da sakon SMS da kashi 40 cikin 100.

“Game da abin da ya shafi data kuwa, za mu so hukumar (NCC) ta koma ta yi amfani da rahoton KPMG don tsayar da farashi kan hada-hadar data.”

Sai dai, da tuni Gwamnatin Tarayya ta nuna rashin amincewarta da yunkurin  kamfanonin.

Gwamnatin ta ce, duk dai kamfanonin sun sanar da ita ta hannun Hukumar NCC kan yunkurin, amma har yanzu ba ta amince musu ba.

Kakakin NCC,  Dokta Ikechukwu Adinde, ya fada wa wakilanmu cewa, “Su kansu kamfanonin sadarwar sun kwana da sanin cewa muna da ka’idojin da akan bi kafin a yi karin kudin sadarwa.

“Kuma har yanzu babu ka’ida ko guda da muka cim ma, ta yaya za su dauko batun karin farashi?

“A yanzu dai babu wani karin farashi da za a yi a masana’antar har sai an cika sharuddan da ke tattare da haka.”

Amma kuma duk da wannan ikirarin da NCC ta yi, ALTON ta ce babu makawa za su yi karin da suka kuduri aniya tare da ba da misalin yadda mambobinta ke fama da tsadar gudanar da harkokinsu a kasar.

A cewar Shugaban ALTON, Gbenga Adebayo:  “Idan gwamnati ba ta shigo ta tallafa wa masana’antarmu ba, babu makawa kamfanonin sadarwa ba su da wani zabin da ya rage musu face su yi karin farashi.

“Matsalar tsaron da kasa ke fuskanta na hana mana gudanar da harkokinmu a wasu wurare yadda ya kamata.”

Sakamakon binciken wakilanmu ya nuna Najeriya na daya daga cikin kasashen Afrika da ke cin moriyar data a kan farashi mai rahusa.

Binciken ya nuna a wasu kasashen Afrika, akan sayar da gibabait daya na data a kan Dala 50, daidai da Naira 27,500.

Amma a Najeriya farashin bai wuce  N2,000 ba, ya danganci kamfanin sadarwar da kuma yanayin tsarin da mutum yake amfani da shi.

Kasashen Malawi, Benin, Chadi da kuma Namibia su ne kan gaba wajen tsadar data a Afrika da ma duniya baki daya.

Sannan Sudan ta kasance mai mafi arahar data inda ake sayar da gigabait daya a kan Dala 0.27.

Abubuwan da ake kyautata zaton su ne suke haddasa tashin farashin data a yankin Afrika har da tsadar harajin da akan dora wa kamfanonin sadarwa, rashin wadataccen kayan aiki da dai sauransu.

Ya zuwa yanzu dai kungiyar masu mu’amala da kamfanonin sadarwa NATCOMS, ta gargadi kamfanonin sadarwar su janye wannan kudurin nasu na neman cilla farashin sadarwa sama.

Shugaban NATCOMS na Kasa, Deolu Ogunbanjo, ya yi kira da kada Gwamnatin Tarayya ta bari hakan ta faru muddin ba so take a kai ’yan Najeriya bango ba.

Ogunbanjo ya nuna girman asarar da kamfanonin sadarwar suka tafka sakamakon rufe layin sadarwar ’yan Najeriya miliyan 71 da aka yi saboda rashin hada lambar wayarsu da ta shaidar dan kasa (NIN).

Don haka, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta duba sannan ta bude ma wadanda lamarin ya shafa layukansu domin taimaka wa kamfanonin sadarwa wajen samun karin kudin shiga ta yadda za su daina tunanin kara farashi.