✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Karin kudin mai: Za mu maka gwamnati a kotu —Jama’ar Funtua

Al'ummar yankin Funtua da kewaye a Jihar Katsina sun yi barazanar maka Gwamnatin Tarayya a kotu idan kara kudin litan man fetur zuwa N340.

Kungiyar ci gaban yankin Funtua da kewaye a Jihar Katsina, ta yi barazanar maka Gwamnatin Tarayya a kotu, kan yunkurin gwamnatin na kara kudin litan man fetur daga N165 zuwa N340.

Kungiyar ta ce idan har Gwamnatin Tarayya ta yi karin kudin mai, al’ummar Najeriya za su kara shiga cikin mawuyacin hali, shi ya sanya ta kuduri aniyar daukar wannan mataki.

Da yake zantawa da Aminiya kan wannna al’amari, shugaban kungiyar, kuma Limamin masallacin rukunin gidajen ’yan majalisar tarayya da ke unguwar Apo a Abuja, Imam Ibrahim Awwal (Usama) ya bayyana cewa sun gama shiryawa da lauyoyinsu kan lallai Gwamnatin Tarayya ta janye shirin nata na kara kukin mai daga N165 zuwa N340, nan da  kwanaki 21, ko kuma kungiyar ta gurfanar da ita a gaban kotu.

Ya ce abin takaici ne yin karin kudin mai, a wannan hali da ’yan Najeriya suke  ciki na  talauci da tsadar rayuwa  da rashin tsaro.

Sannan kullum ana kara ciyo bashi.

“Shugaban kasa ya yi alkawarin zai magance zaluncin da ake yi wa talakawan Najeriya.

“Don haka wasu matan sun haihu a layin zaben shi, wasu sun yi hadari sun rasa rayukansu, saboda murnar ya ci zabe.

“Sannan ya zo yanzu ya ce zai yi karin kudin mai, a wannan hali da ake ciki.

“Wannan karin kudin mai zai dada jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali.

“Don haka muna  kira ga gwamnati ta dakatar da wannan kuduri nata, na kara kudin mai a Najeriya ko kuma mu gurfana da ita a gaban kotu.”