✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin kudin mai zai jefa karin ’yan Najeriya cikin talauci —Abdulsalami

Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa ta ba da shawarar kara farashin litar man fetur zuwa N302

Tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, ya gargadi Gwamnatin Tarayya kan yunkurinta na kara farashin man fetur.

Abdulsalami ya yi gargadin ne bayan Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa ta ba da shawarar kara farashin litar man fetur zuwa N302, wanda tuni ya jawo ce-ce-ku-ce.

Da yake bayanin nasa a wurin Babban Taron Tattaunawa na Daily Trust Karo na 19 a ranar Alhamis, 20 ga Janairu, 2022 a Abuja, Abdulsalami ya ce karin farashin man zai jefa karin ’yan Najeriya a cikin talauci.

Duk da cewa kwamitin wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, yake jagoranta ya bayar da shawarar kara farashin a watan  Nuwamba, a halin yanzu dai farashin man fetur N162 zuwa N165 ne a Najeriya.

Yunkurin kara farashin man na daga cikin matakan da Gwamnatin Tarayya take dauka na janye hannunta a harkar gudanar da bangaren man fetur da kuma bayar da tallafi a kansa.

Majalsiar, wadda Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yake jagorantar karamin kwamitin da ta kafa a kan lamarin, ta mika rahoton ne a wani zama da suka yi da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), a kan farashin man fetur da ya dace a sa a Najeriya.

“Kwamitin ya riga ya karba ya kuma amince da rahoton wanda ya ba da shawarar kara farashin fetur da N130 zuwa N140 zuwa watan Fabrairun 2022.

“Ya kuma bukaci manyan masu sayar da fetur su rika sanar da farashin a wasu ayyanannun shafukan intanet da manhajojin waya, akalla minti 15 kafin kara farashin.

“Yin hakan zai rage wa gwamnati asarar Naira biliyan 250 da take yi a duk shekara, ragowar biliyan N195 kuma za a ba wa ’yan Najeriya tallafi da su,” inji rahoton.

Rahoton TheCable ya ce tun bayan sanarwar da Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta yi cewa gwamnati za ta janye tallafin a watan Yuni ake ta fargabar yiwuwar karin farashin man fetur.

Sai dai bayan wata ganawa da suka yi da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya ce Buhari ya tabbatar masa cewa bai ba wa kowa damar janye tallafin ba.

An nemi jin ta bakin Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, a kan lamarin, amma ya ce, “Game da cire tallafi, ina ganin za ku ba ni lokaci, in tuntubi hukumomin da suka dace tukuna.