Karin lokacin zirga-zirgar Keke NAPEP a Yobe | Aminiya

Karin lokacin zirga-zirgar Keke NAPEP a Yobe

    Idriss M. Idriss

Fatar alheri ga Aminiya. Don Allah ku ba mu dama mu yi kira ga Gwamnan Jiharmu ta Yobe Alhaji Mai Mala Buni. Don Allah Gwamna ka taimaka ka kara mana lokacin zirga-zirgar Keke NAPEP a garuruwan Damaturu, Potiskum da Gashuwa, koda zuwa karfe 10 na dare ne. Wallahi dokar karfe 6 na yamma ta ishe mu haka. Yau kusan shekara 5 ke nan muna ta fama, kuma sanin kowa ne cewa an samu zaman lafiya a gruruwanmu. Mai girma Gwamna wallahi a birnin Maiduguri ma dokar Keke NAPEP karfe 11 na dare ne balle Damaturu. Saboda haka muna kira da babbar murya ga Gwamnanmu Mai Mala ya taimaka ya duba wannan bukata ta talakawansa.

Daga Idriss M. Idriss, Damaturu Jihar Yobe, 08033775767.