✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin mutum miliyan bakwai sun fada talauci a Najeriya —Bankin Duniya

A bayan nan ne Buhari ya ce gwamnatinsa ta fitar da mutane miliyan 10 daga kangin talauci.

Bayan kwanaki uku da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar cewa gwamnatinsa ta fitar da mutane miliyan 10 daga kangin talauci, Bankin Duniya ya ce hauhawar farashin kayayyakin abinci ya jefa mutum miliyan bakwai cikin talauci.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce hauhawar farashin ya ragu da kashi 0.19 cikin 100 a cikin watan Mayu na bana,  inda ’yan Najeriya ke ci gaba da korafi kan tsadar bukatun yau da kullum kamar abinci da magunguna da sauran kayayyakin masarufi.

Masana sun ce alkaluman Bankin Duniya bai ba su mamaki ba, idan aka yi la’akari da cewa hatta hukumar kididdiga ta gwamnatin kasar NBS ta sha yin bayyanan hauhawan farashi a watannin da suka gabata dangane da ya sanya tsadar kayayyakin masarufi.

A cikin wata sanarwa da Bankin Duniya ya fitar ranar Talata a Abuja, ya ce: “Farashin abinci ya kai sama da kashi 60 cikin 100 na jimillar karuwar hauhawar farashin kaya.”

Sanarwar ta ce hakan ya yi sanadiyar jefa ’yan Najeriya kimamin miliyan bakwai cikin kangin talauci a shekarar 2020 da ta gabata.

Sanarwar da mai magana da yawun bankin, Mansir Nasir ya sanya wa hannu ta ce yayin da gwamnati ke daukar matakan tayar da komadar tattalin arzikin, akwai bukatar a tsara manufofi masu inganci don murmurewa.

Wani masanin tattalin arziki Dr Isa Abdullahi na Jami’ar Kashere ya danganta hauhawan farashin da matsalar da aka samu wajen aikin noma sakamakon yadda rikice rikice da hare haren Yan bindiga suka hana manoma zuwa gonakin su da kuma matsalar ambaliya da sauyin yanayi.

A cewarsa, yayin da wasu daga cikin wadannan matsaloli mutane ne ke haddasa su, akwai bukatar hukumomi su tashi tsaye wajen samar da tsaron da manoma za su koma gonakin su domin samar da abinci da kuma rage dogaro da shigowa da shi daga kasashen duniya.