✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin ’yan matan Chibok sun tsere daga hannun Boko Haram

Jama'a na ta tururuwa zuwa gidan iayyen daliban don taya su murna.

Rahotanni sun bayyana cewa karin daliban makarantar Chibok da ke Jihar Borno da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su tun sun tsere daga hannun mayakan.

Wakilin Aminiya ya samu bayanan da ke nuna cewa akwai alamun daliban sun tsere ne a ranar Alhamis, 28 ga Janairu, 2021.

Daya daga cikin iyayen daliban makarantar ya shaida wa wakilinmu cewa jami’an kula da batun yaran sun tuntubi iyayen daliban kuma akwai yiwuwar nan gaba za a gayyace zuwa Maiduguri.

Wata majiyar ta ce ana kyautata zaton daya daga ’yan matan mai suna Halima Ali ta tsere ne bayan shekara biyar da tserewar ’yar uwarta Maryam daga hannun kungiyar.

Halima na daga cikin daliban da aka gano cewa shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya ba da uamrnin a aurar da ita ga wani kwamandan kungiyar, ’yan watanni bayan an yi garkuwa da su.

Aminiya ta yi kokarin tattaunawa da mahaifinta, Ali Maiyanga amma hakan bai yiwuw, sai dai wata majiya ta tabbar wa Aminiya cewa abokan arziki na ta yin tururuwa zuwa gidan domin taya su murna game da albishir din.

Sakataren Kungiyar Iyayen Daliban Makarantar Sakandaren ta Chibok, Lawal Zannah ya ce sun samu labari cewa wasu daliban sun tsere daga hannun kungiyar, amma babu bayanin adadinsu.

“Mun samu labarin cewa wasu daga cikin daliban sun tsere a dajin amma babu bayani game da adadinsu,” inji shi.

A shekarar 2014 ne mayakan Boko Haram suka kai hari makarantar suka yi garkuwa da dalibai 219.

Daga baya hudu daga cikinsu suka tsere kafin kungiyar ta sako karin 21 da kuma 82, wanda ya kai adadin 107.