Daily Trust Aminiya - Kariya daga Ciwon Shanyewar Barin  Jiki
Subscribe

Kariya daga Ciwon Shanyewar Barin  Jiki

Mene ne gaskiyar cewa wai hawan jini ne ke kada mutum ya kawo shanyewa ko mutuwar barin jiki? Kuma idan haka ta faru ana warkewa?

Amsa: Eh, hawan jini shi ne babba a jerin abubuwan da ke kawo shanyewar wani bangare na jiki, amma akwai sauran abubuwa ban da hawan jinin. Ga yadda abin yake: Bugun jini a kwakwalwa shi ne kan kawo ciwon shanyewa ko na mutuwar barin jiki. Ciwon dan uwa ne ga bugun zuciya, wanda shi kuma bugun jini ne na zuciya.

Shi wannan ciwo yakan auku ne yayin da wata matsala ta faru a cikin magudanan jini na wani bangare na kwakwalwa wanda alhakin motsa bangaren jiki ya rataya a wuyansa. Wannan matsala sanadinta dayan-biyu; imma dai sanadiyar toshewar magudanar jinin ko kuma sanadiyar fashewa. Abubuwan da kan kawo toshewar sun hada da gudan jini ko kitse. Su kuma abubuwan da sukan kawo fashewar sun hada da hawan jini mai tsanani, bugun kai na hadurran abin hawa ko sanadiyar wani tsoro. Haka nan shanyewar barin jikin kan iya faruwa idan aka samu kumburin sashen kwakwalwar da alhakin motsa bangaren ya rataya a wuyansa, kamar a buguwa na hadari har ila yau.

Idan daya daga cikin wadannan ya faru, bangaren kwakwalwa na wannan wuri kan rasa jini, don haka sai a samu alamu iri-iri. Alamun sukan dauki nau’in jin matsanancin ciwon kai, ko yanke jiki a fadi farat daya kamar yadda ka ce, idan an zo tashi a kasa, bayan haka a kasa daga ko motsa wani sashe na jiki kamar kafa ko hannu, na bangaren dama ko na hagu, amma ba a samun dukkan bangarorin lokaci guda. Idan aka samu cewa dukkan bangarorin dama da hagu ne suka shanye to ba ciwon shanyewar barin jiki ba ne, wani ciwo ne na daban, tunda akwai cututtukan da kan sa shanyewar dukan barin jiki biyu, wadanda su ba a sa su a nan. Sauran alamomin sun hada da kasa magana ko nauyin yin magana ko fuska da baki su karkace, ko a samu dukkan wadannan abubuwa da aka lissafa ko a samu kusan dukkansu a lokaci guda.

Wadanda suke cikin hadarin samun wannan matsala ban da masu hawan jini akwai mutane masu kiba sosai, sai mutane masu shan taba sigari na tsawon lokaci, sai masu shan barasa, sai marasa motsa jiki, sai masu matsalar hawan jini ko ciwon zuciya. Yakan iya  aukuwa ga masu yawan shekaru, wato wadanda suka fara tsufa, sai mata masu matsalar ciwon kai na bari guda da wadanda aka dora a kan kwayoyin hutun haihuwa.

Hanyoyin kariya:

Ba wai ana zayyana wadannan matsaloli ba ne domin a tsorata mutane, a’a hasali ma bincike ya nuna cewa yawan fadakar da jama’a da sanar da su ire-iren abubuwan da suke hadarin kamuwa da shi, kan rage tsoro da fargaba da rashin sanin abin da zai faru da abin yi idan hadarin ya faru, kuma yakan taimaka wa jama’a su san yadda za su shawo kan matsalar.

Wadanda suke cikin hadarin kamuwar, ya kamata ke nan a kullum su kwana da shirin kiyaye wannan. Wadannan hanyoyi kuwa su ne:

 1. Yawan bincikar hawan jini a kalla sau daya a shekara ga duk wanda ya ba shekara hamsin baya.
 2. Masu matsalar hawan jini kuma wadanda suka riga suka fara shan magani, su rika tabbatarwa suna bibiyar matakin hawan jinin nasu, musamman ta sayen na’urar hannu don aunawa a gida akalla sau daya a duk mako.
 3. Masu shan taba sigari su yi kokarin dainawa.
 4. Masu shan barasa tunda suna cikin hadarin, su hakura da ita.
 5. Masu kiba su nemi hanyoyin da za su bi domin rage kiba, kamar rage yawan cin abinci, rage zaki da maiko, hada kayan ganye da na marmari masu yawa a abinci da yawan motsa jiki.
 6. Matan da aka dora a kan kwayoyin tsara iyali, tunda suna cikin hadarin samun kiba da hawan jini sakamakon kwayoyin, yana da kyau su rika yawan bibiyar kibarsu da matakin hawan jini.
 7. Mutum ko yana da kiba ko ba ya da ita, yana da kyau ya samu wani nau’i na motsa jiki wanda zai iya dauwama ko dorewa da yi akalla ranaku uku ko hudu cikin mako.
 8. Babbar hanyar da aka sani mai kawo saukin wannan matsala idan ta riga ta faru, ita ce ta hanzarin samun taimakon asibiti, wato cikin awanni biyun farko na samun matsalar. Idan aka zauna da matsalar tsawon yini ko dare ba a samu taimakon magani da gashi ba, abin ta’azzara yake. Kamar yadda ka tambaya, wadansu shanyewar tasu da kanta takan gyaru idan aka samu budewar magudanar jinin da ta toshe. Wadansu kuma sai an dade ana shan magunguna da bibiyar gashi da atisaye, wadansu kuma ba sa warkewa, wato bangaren da ya shanye ya mutu ke nan har abada komai magani.
 9. Idan mutum na cikin hadarin samun wannan matsala sosai da sosai kamar mai hawan jini da matsalar shan taba da ya kasa bari, ko yana da kiba a jikinsa shi kadai, (domin akwai irinsu da dama), to ya tabbata ya tattauna batun hadurran duk da likitansa domin watakila ya dora shi a kan wasu magunguna na kiyaye aukuwar bugun jinin.

Shin da gaske ne sanya danyen tufafi a jiki kamar singileti yana da illa ga lafiya?

Daga Saminu Artillery, Yelwan-Shendam

Amsa: Idan kana nufin danye kamar jikakke ne, haka ne, musamman idan yanayin da sanyi-sanyi ko danshi-danshi hakan zai iya kawo mura.

Ni maigidana ne idan ya sha ruwan sanyi sai ya ji kamar yana kwarara masa a kunnuwa, kunnuwan su rika kaikayi. Ko me ke kawo haka?

Daga Maryam A.

Amsa: A’a ba dai ruwan ba sai dai danshin sanyin. Kin san a saman makoshi akwai kofofin da suka bude zuwa kunnuwa biyu. Ana kyautata zaton danshin sanyi ne, domin wani ma ya taba tambayar wai idan ya sha ruwan sanyi yakan ji kamar ruwan ya shigar masa cikin zuciya. Amma idan ya tabbatar ruwan ne ke shiga kofofin kunnuwan, to fa sai ya ga likitan kunne ya duba wurin.

More Stories