✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karon farko tawagar mata ta Ingila ta lashe gasar Nahiyar Turai

An kafa wannan gasar ta mata a shekarar 1969, wadda Jamus ta lashe sau takwas a tarihi.

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta mata ta Ingila ta samu nasarar lashe gasar nahiyar Turai ta Euro 2022, wanda shi ne karonta na farko a tarihi.

Nasarar da tawagar Ingilar ta samu na zuwa ne bayan ta doke takwararta ta Jamus 2-1 a wasan karshe na gasar da aka buga a filin Wembley da ke Ingila.

Ingila ce ta fara cin kwallo ta hannun ‘yar wasar tawagar, Ella Toone, sai kuma Lina Magull ta ci wa Jamus a minti na 79, wanda hakan ya sa wasan ya kare a kunnen doki a mintuna 90 da suka kwashe suna fafatawar a tsakaninsu.

Hakan ya sa aka kara yawan mintuna 30, inda ana tsaka da gumurzu ‘yar wasar Ingila, Chloe Kelly, ta jefa kwallo ta biyu a minti na 110 a ragar Jamus.

An kafa wannan gasar ta mata a shekarar 1969, wadda Jamus ta lashe sau takwas a tarihi.

Wannan ce ta sa ake ganin tawagar ta Jamus a matsayin gagara tsara a gasar ta mata, don baya ga haka, sau biyu tana lashe Kofin Duniya, sannan kungiyoyin da ke wakiltar kasar sun lashe gasar zakarun Turai sau tara, adadin da ya zarce na kowacce kasa.