✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Karshen fadan Kumurci da Mesa, mutuwar kasko

Karshen fadan kumurci da mesa, mutuwar kasko.

Kumurci da mesa macizai biyu ne masu hatsarin gaske.

Yayin da kumurci ke takama da dafi mai karfi wanda duk halittar da ya ciza ko ya sara ba ta kai labari, ita kuwa mesa karfi take takama da shi ba dafi ba.

Fadan wadannan halittu biyu abin babu kyau in ji masana, saboda a karshe kowannensu kan rasa ransa.

A cewar masanan, idan mesa ta hadu da kumurci za ta so ta farauce shi ta hadiye a matsayin abincinta, haka ma kumurci, ba zai kyale mesa ba idan ya san zai samu nasara a kanta.

A duk lokacin da fada ya kaure a tsakaninsu, kumurci kan yi kokarin kai wa mesa cafka, musamman a wuya, ya kafa hokaransa ya rike sannan ya zuba dafi.

Ta haka dafin zai gangara a hankali ya baje zuwa sassan jikin mesar ya kassara ta.

Ita kuwa mesa, takan tabbatar kafin dafin kumurcin ya kassara ta, ta kanannade kumurcin ta matse shi ta yadda ku numfasawa ba zai iya ba balle kuma ya kwaci kansa.

Wannan ke sa a karshen lamari, mesar ta mutu saboda dafin kumurci, kumurci kuwa ya rasa ransa saboda makarar mesa da ya sha.

A nan, sai a yi mutuwar kasko, mesa ba ta hadiye kumurci ba, haka kumurci bai karu da mesa ba.