✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karuwai sun lakada wa matar aure duka a gaban mijinta

Sai da aka kai matar asibitin bayan abin da ya faru a wani otel.

Wata matar aure ta sha da kyar a hannun wasu karuwai da suka yi mata taron dangi suka lakada mata dukan tsiya.

Lamarin ya auku ne a lokacin da wannan mata ta je neman mijinta a wani otel da ke daya daga cikin manyan tashoshin mota da ke birnin Badun, hedikwatar Jihar Oyo.

Saboda wasu muhimman dalilai, mun boye sunan majiyar da ta ba mu wannan labarin da sunayen matar da mijinta da sunan otel da tashar.

Majiyar mai tushe, wadda ta ce da yawun shugabannin tashar ta yi wannan bayani, ta shaida wa Aminiya cewa, “Wannan matar aure Bahaushiya ce ta samu labarin cewa mijinta, wanda shi ma Bahaushe ne, yana zuwa wani otel yana kwana a dakin karuwa idan ya koma gida yana yi mata karyar cewa hada-hadar kasuwanci ce take hana shi komawa gida.

“Saboda yawaitar lamarin ne a karo na farko matar ta yi tattaki daga gidanta zuwa wannan otel inda take zargin mijinta da tarewa a dakin karuwa bayan ya bar ta da ’ya’ya uku.

“Ta tabbatar da zargin nata bayan ta yi ido biyu da mijinta kwance a dakin karuwa, inda ta koma gida cikin kuka da hawaye ba tare da ta yi wa mijin bayanin komai ba.

“Amma bayan tafiyarta ne ita karuwar ta ja kunnensa da ya daina zuwa wurinta saboda guje wa fada a tsakaninsu.”

Majiyar ta kara da cewa, “Mutumin bai daddara ba ya ci gaba da zuwa kwanan-gida a dakin wannan mata mai zaman kanta.

“Sai a karo na biyu da matar mutumin ta sake komawa wannan otel inda ta yi kokarin saka shi a gaba zuwa gida amma ya ki yarda.

“Hakan ne ya sa matar tasa ta fusata ta fara dukan daya daga cikin karuwan, su kuma suka mayar da martani ta hanyar yi mata taron dangi suka lakada mata dukan tsiya.

“Wannan matsala ta kai ga ofishin ’yan sanda wadanda suka garzaya da ita zuwa asibiti domin yi mata maganin raunukan da ta yi.

“Shugabannin tashar sun hanzarta daukar matakin sasanta lamarin ta hanyar tilasta wadannan mata masu zaman kansu daukar nauyin biyan kudaden jinyar wannan mata da jan kunnen mutumin cewa kada a sake ganin shi a cikin wannan otel, tare da bayar da hakuri ga matarsa da iyayenta su koma gida su kara daukar matakin sulhunta miji da matar domin zama lafiya.