✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karuwanci: An ceto ’yan mata 22 da aka killace a otal a Ogun

An kawo ’yan matan ne daga jihar Akwa Ibom domin yin sana’ar ta karuwanci a cikin otal din.

Jami’an ’yan sanda a jihar Ogun sun ceto wasu ’yan mata 22 wadanda aka yi zargin an ribace su daga jihar Akwa Ibom zuwa jihar domin sana’ar karuwanci.

Kakakin rundunar, Abimbola Oyeyemi ne ya tabbatar da hakan ga ’yan jarida a Abeokuta babban birnin jihar ranar Asabar.

Ya ce a kan kawo ’yan matan ne daga wasu jihohin domin yin sana’ar ta karuwanci a cikin wani otal dake garin Itele Ota a Karamar Hukumar Ado Odo-Ota ta jihar.

Abimbola ya ce Baturen ’Yan Sanda na yankin na Ota, ACP Muhideen Obe ne ya jagoranci kai samame zuwa otal din bayan sun sami rahotannin sirri kan cewa an killace ’yan matan wadanda ke tsakanin shekaru 10 zuwa 14 a cikinsa.

Ya ce, “Bayan mun titsiye su, ’yan matan sun shaida mana yadda aka yi musu romon kunne aka raba su da kauyukansu dake jihar Akwa Ibom zuwa Ogun, tare da alkawarin samar musu da aiki a shagunan sayar da abinci da manyan kantina.

“Amma abin takaici, sai aka bige da kai su Legas, daga can kuma aka karkatar da akalarsu zuwa otal din a jihar Ogun a matsayin karuwai.

“Sun kuma shaida mana cewa an hana su amfani da wayoyinsu na salula, lamarin da ya hana su damar sanar da iyayensu da sauran ’yan uwa halin da suke ciki,” inji kakakin.