Karuwar ta’ammali da kwayoyi na da alaka da yajin aikin ASUU — Obaseki | Aminiya

Karuwar ta’ammali da kwayoyi na da alaka da yajin aikin ASUU — Obaseki

Godwin Obaseki, Gwamnan Jihar Edo
Godwin Obaseki, Gwamnan Jihar Edo
    Usman A. Bello, Benin da Sani Ibrahim Paki

Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce karuwar matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi a Jihar na da alaka da yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ke ci gaba da yi.

Ya bayyana matsalar shan kwayar a matsayin babban kalubalen tsaro na biyu mafi girma bayan hatsarin mota a Jihar.

A cewar Gwamnan, Jihar ta fuskanci ta’ammali da kwayoyi har sau 19 a watan Fabrairu, sai sau 34 a watan Maris da kuma sau 23 a watan Afrilu.

Obaseki ya bayyana hakan ne a karshen mako bayan kammala taron Majalisar Tsaro ta Jihar tare da hukumomin tsaron da ke Jihar.

Ya ce, “Ta’ammali da miyagun kwayoyi na kan gaba cikin abubuwan da suka fi kawo mana kalubalen tsaro a jiharmu.

“Bincikenmu ya gano cewa a ’yan watannin nan, an samu karuwar matsalar, wanda hakan ba zai rasa nasaba da yajin aikin ASUU ba wanda ya tilasta wa dalibai zaman gida ba tare da yin komai ba.”

Ya ce sun yi ittifakin yajin aikin na taka muhimmiyar rawa wajen kara damalmalewar al’amura.

Daga nan sai Gwamnan ya roki ASUU da Gwamnatin Tarayya da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun janye yajin aikin ko don daliban.

“Duk wanda yake zaman kashe wando babu abin da ba zai iya aikatawa ba. Daya daga cikin hanyoyin da zamu bi wajen rage ta’ammali shi ne matasan nan su koma makaranta,” inji Obaseki.

Da yake mayar da martani a kan lamarin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Mista Abutu Yaro, ya ba da tabbacin cewa jami’an tsaro za su ci gaba da yin duk kokarinsu wajen inganta harkokin tsaro a Jihar.