✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karyewar gada ya jawo asarar rai a Zariya

Gadar ta karye ne sakamakon mamakon ruwan sama

Ana fargabar mutum daya ya rasu sannan gonaki da dama sun lalace a yankin Maliki da ke cikin karamar hukumar Zariyan jihar Kaduna da yammacin Talata.

Idan za a iya tunawa, an samu ruwan sama mai yawa a baya-bayan nan a wasu sassan Zariya da kewaye, lamarin da ya haifar da cikas ga rayuwar al’ummar yankin.

Gidaje da gonaki masu yawa ne suka lalace sakamakon mamakon ruwan saman.

Da yake karin kaske kan batun, Kakakin Yammacin Zazzau, Mutawakkilu Yusuf Rafin Yashi, ya ce ruwa ya mamaye tare da karya gadar Maliki zuwa Kafin Mardani wadda ta hada kauyuka sama da 20 a shiyyar yammacin Zariya.

Yusuf ya shaida wa wakilinmu cewa marigayi Alhaji Awwal Balarabe ya cim ma ajalinsa ne a hanyarsa ta komawa gida bayan ya dawo daga harkokinsa kamar yadda ya saba a Zariya.

Ya ci gaba da cewa, ganin yadda ruwa ya cika gadar ya tumbatsa, sai marigayin ya yanke shawarar ajiye motarsa sannan ya tsallake da kafa don ya karasa gida ba tare da sanin gadar ta karye ba.

Ya ce jefa kafar Alhaji Awwal kan gadar ke da wuya, sai ruwan ya ja shi ya tafi da shi.

A cewar Kakakin na Yammacin Zazzau, da safiyar Laraba ce aka gano gawar marigayin kuma tuni ka yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kawo yanzu matasan yankin sun yunkura da aikin gayya don gyara gadar.