✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari da Osinbajo za su ci abincin N167m a 2021

Buhari zai kashe N98,306,492 a kan abinci da karbar baki, Osinbajo kuma N50,888,210

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo za su kashe N167,459,107 kan abinci da kayan makwalashe a shekara ta 2021.

Hakan na kunshe ne a daftarin kasafin kudin da shugaban ya gabatar wa da Majalisar Dokoki ta Kasa ranar Alhamis din da ta gabata.

Yayin da shugaban zai kashe N98,306,492 a kan abinci da karbar baki, an ware wa mataimakin nasa N50,888,210 domin hakan.

Bugu da kari, Fadar Shugaban za ta kashe N116,194,297 domin sayen tayoyin motoci masu silke, sabbin motoci, motocin daukar mara sa lafiya da ma wasu motocin na zirga-zirga.

A jimlace, an ware wa Fadar Shugaban Kasa da sauran Gidan Gwamnati Naira 72,918,449,739 a kasafin na 2021.

Daga cikin adadin za a kashe N24,344,026 domin ci gaba da aikin kawata lambun Fadar Shugaban Kasa da kuma gina karamin wurin ajiye namun daji.

Aikin shuke-shuke da kula fulawoyi zai lashe N15,924,777, yayin da aikin ban-ruwa da dasa sabbin ciyayin alfarma zai ci N436,264,142.

Sauran ayyukan da aka ware wa kudaden sun hada da sayo sababbin karafunan motocin fadar da gyare-gyarensu a kan N4,854,381,299 sai kuma N389,645,942 na biyan bashin ragowar gyaran ababen hawan da aka yi tun daga 2016.