✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasafin fanshon tsoffin sojoji na cikin garari —MPB

Hukumar fanshon sojoji ta ce zaftare N27bn a kasafinta 2021 zai yi wa tsoffin sojojin babbar illa.

Hukumar kula da Fanshon  Sojoji ta Najeriya (MPB) ta bukaci Majalisar Tarayya ta kara kason da aka ware wa tsoffin sojoji a kasafin 2021.

Da yake kare kasafin hukumar a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa, Shugaban MPB, Commodore Saburi Lawal ya ce kason da aka ba wa tsoffin sojoji a kasafin ya yi kadan matuka.

“Muna rokon kwamitin ya kara adadin kudin da Ofishin Kasafi na Tarayya ya gabatar domin biyan kudaden sallama, fansho, da hakkokin mamata da sauransu ya koma daidai yadda hukumar ta gabatar.

“Halin da ake ciki a Arewa maso Gabas ya sa ana samun yawan mamata kuma yanzu mutane na yawaita yin ritaya sannan akwai bukatar biyan hakkokin ‘yan fanshon da ke bin bashi”, inji shi.

Commodore Saburi Lawal ya ce cire Naira biliyan 27 daga N216,48,604,822 da MPB ta gabatar da farko zai hana a iya biyan fanshon tsoffin sojoji da kudaden sallamar wadanda suka yi ritaya da kuma hakkokin wadanda suka rasu da sauran bukatun hukumar.

Ya shaid wa kwamitin cewa rage kasafin hukamar zuwa N183,748,495,159 da Ofishin Kasafi na Tarayya ya yi zai jefa hukumar cikin tsaka mai wuya.

A jawabinsa bayan rokon da hukumar ta yi, shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wamakko ya yi alkawarin yin nazari a kan bayanin da hukumar ta yi.